Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sa'udiyya Ta Sake Yi Wa Isra'ila Tayin Cikakken Zaman Lafiya Idan Ta Janye - 2002-03-10


Sa'udiyya ta sake yi wa Isra'ila tayin kulla zaman lafiya da kasashen Larabawa idan ta janye daga yankunan Larabawa da ta mamaye a yakin 1967.

A lokacin da yake magana yau lahadi a birnin al-Qahira, ministan harkokin wajen Sa'udiyya, Sa'ud al-Faisal, ya ce Isra'ila zata samu abinda ya kira "cikakken zaman lafiya" da kasashen Larabawa idan har ta amince da wannan shawara ta hukumomi a birnin Riyadh.

Al-Faisal, wanda tun farko ya gana da shugaba Hosni Mubarak na Misra, ya bai wa 'yan jarida karin bayani fiye da duk wani lokaci a baya kan shawarar zaman lafiyar da Sa'udiyya ta gabatar a watan da ya shige.

Wannan shawara ta Sa'udiyya tana daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna kansu a taron kwanaki biyu na ministocin harkokin wajen kasashen larabawa a al-Qahira, wanda aka gudanar a daidai lokacin da ake ci gaba da tashin hankali tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Ministan harkokin wajen na Sa'udiyya ya ce a shirye kasashen larabawa suke su kulla cikakken zaman lafiya mai dorewa tsakaninsu da Isra'ila, amma kuma ya ce tilas ne Isra'ila ta nuna kyakkyawar aniyarta ta hanyar janyewa daga yankunan Larabawa dake hannunta tare da yin na'am da bukatun halal na Falasdinawa, ciki har da kafa kasarsu mai hedkwata a birnin Qudus.

XS
SM
MD
LG