Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce Sun Shiga Mataki na Biyu na Yaki da Ta'addanci - 2002-03-11


Shugaba Bush ya ce Amurka da kawayenta sun shiga mataki na biyu na yakin da suke yi da ta'addanci, yakin da a cikinsa suke so tilas su tabbatar da ganin 'yan ta'adda sun rasa mafaka.

Shugaba Bush ya yi wannan furuci ne a fadarsa ta White House, a wajen wata hidima ta juyayin cika watanni shidda da hare-haren ta'addancin da aka kawowa Amurka.

Shugaban ya lashi takobin cewa tilas ne a maida kowane dan ta'adda tamkar mujiya a duniya. Yayi alkawarin cewa duka kasashen duniya za su dauki matakan diflomasiya da na kudi da kuma na soji akan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Tutocin kasashen duniya kimanin 170 ne ke kadawa a bayan shugaban, lokacin da yake tsaye, an yi haka ne a wani mataki na karrama kasashen dake cikin yakin da ake yi da ta'addanci wanda aka fara fafatawa ga watanni shidda kenan.

Mr.Bush ya ambaci sunayen kasashen Jamus da Denmark da Afghanistan a zama kasashen da suka sadaukar da rayukan sojojinsu a cikin burin cimma nasarar wannan yaki.

Haka nan kuma an yi hidimomi a jihohin New York da Pennsylvania. Jakadan Najeriya a nan Amurka, Farfesa Jibril Aminu, na daga cikin manyan jami'an da suka halarci hidimar ta fadar White House. Profesa Jibril Aminu ya yi jawabi a fadar ta White House.

XS
SM
MD
LG