Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitaccen Tarihin Robert Mugabe - 2002-03-13


To shi dai Robert Mugabe, shugaban na Zimbabwe da ya sake lashe zaben, ya fara baiyana a fagen harkokin siyasar duniya ne a lokacin yakin kwatar 'yancin kasarsa a cikin shekarun 1970, a lokacin fafutukar kubutar da kasar daga mulkin tsirarun turawa. To amma yanzu wasu suna daukarsa a zama mai mulkin danniya da zalunci.

Dan shekaru 78, Mr. Mugabe ya taba zama shugaban wata kungiyar sari-ka-noke mai ra'ayin Markisanci a lokacin yakin da aka yi a tsohuwar kasar ta Rhodesia.

A shekarar 1979 da 1980, bayan yakin sari-ka-noke da kwanton-bauna na tsawon shekaru 7, shugaba Mugabe da daya madugun kwatar 'yancin bakaken fatar kasar, wato marigayi Joshua N'Komo, sun kulla wani shirin mayar da kasar bisa mulkin bakake masu rinjaye, al'amarin da ya daga darajar sabuwar kasar ta Zimbabwe a idanun duniya.

A matsayinsa na bakar fata na farko da ya zama shugaban sabuwar gwamnatin kasar ta Zimbabwe a farkon shekarun 1980, Mr. Mugabe ya rungumi manufofin Makisanci. To amma kuma a lokaci guda ya yi kokarin baiwa tsirarun turawa manoma tabbaci tare da karfafa musu guiwar bayar da taimakonsu a kokarin gina sabuwar kasar.

To amma sai ya fara kuntatawa magoya-bayan babban abokin adawarsa, Joshua N'Komo. A cikin shekarar 1982, jami'an tsaron kasar sun kai samame a tungar Mr. N'Komo ta Matabeleland, inda suka kashe dubban fararen hula.

Mr. Mugabe ya zama cikakken shugaban kasar ta Zimbabwe na biyu a shekarar 1987, inda ya ci gaba da aiwatar da manufofinsa na gurguzu. To amma kuma wargajewar tsohuwar Tarayyar Sobiyat ta tilasta masa ya takaita burorinsa na zamar da Zimbabwe kasa mai amfani da jam'iyyar siyasa guda daya, wato kasar 'yan kwaminis.

A shekarar 2000, mummunar matsalar tabarbarewar tattalin arziki da kuma bakin jinin da gwamnatinsa ta yi wajen tsoma hannu a yakin basasar kasar Congo-Kinshasa sun kara tsaurara adawa ga mulkin Mr. Mugabe.

Wannan ya sanya gwamnatinsa ta fara daukar matakan kuntatawa tare da yin tarzoma ga manoma fararen fata da alkalai da 'yan adawa. Mr. Mugabe ya shirya kwace akasarin gonakin jajayen fatar kasar domin rabawa ga bakaken fata manoma matalauta wadanda sune suka fi rinjaye a kasar kuma sune suka fi bashi goyon-baya.

Tun daga lokacin sai Morgan Tsvangirai shugaban jam'iyyar adawa ta MDC ya fara kalubalantar Mr. Mugabe, saboda shi Tsvangirai ba ya son ganin kananan manoma bakaken fata sun mallaki gonaki. Wannan ya sanya ya shiga takarar zaben shugaban kasar da gudanar a ranaikun 9 da 10 da 11 ga wannan Wata na Maris, zaben da Mr. Mugabe ya lashe da gagarumin rinjaye, amma kuma Mr. Tsvangirai ya ce an tufka gagarumin magudi.

Kasashen turawa na yammacin duniya ma sun soki lamirin yadda aka gudanar da zaben. To amma a tattaunawar da ya yi da sashen Hausa na VOA, shugaban tawagar jami'an Kungiyar ECOWAS masu kallon zaben ya ce, ba su ga alamar aikata wani magudi ba.

XS
SM
MD
LG