Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Na Ci gaba da Kame Ramallah - 2002-03-13


Sojojin Isra'ila sun ci gaba da kame birnin Ramallah na Palasdinawa, kwana guda bayan da wasu hare-hare biyu a Yammacin kogin Jordan da zirin Gaza suka hallaka Palasdinawa fiye da 30.

An ci gaba da caba fada jefi-jefi a Ramallah, a lokacin da sojojin Isra'ila suka karade birnin suna neman Palasdinawa 'yan gwagwarmayar kwatar 'yancin kai da kuma makamai.

An bada rahoton cewa a yau laraba sojojin Isra'ila sun kashe mukaddashin kwamandan jami'an tsaron lafiyar shugaban Palasdinawa Yasser Arafat, tare da wani dan kasar Italiya dan jarida mai daukan hotuna mai zaman kan shi.

Da jijjifin jiya talata sojojin Isra'ila tare da tankokinsu na yaki, sun mamaye Ramallah da sansanin 'yan gudun hijirar Jabaliya dake zirin Gaza, al'amarin da ya janyo kazamin fada da bindigogi tsakaninsu da Palasdinawa 'yan bindiga.

Isra'ila ta ce an kai harin ne da aniyar kakkabe Palasdinawa masu gwagwarmayar kwatar 'yancin kansu, wadanda ake zargi da shirya hare-haren kunar-bakin-wake da sauran hare-hare kan 'yan Isra'ila.

XS
SM
MD
LG