Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Indiya Ta Hana 'Yan Hindu Yin Taron Addini A Wurin Da Ake Rikicinsa - 2002-03-13


Madaukakiyar kotun kasar Indiya ta haramtawa masu kishin addinin Hindu yin addu'o'i a kusa da inda aka rushe wani Masallaci mai tarihi, wanda aka gina tun a cikin karni na 16, a garin Ayodhya dake arewacin kasar.

Ayarin wasu alkalai ukku ne ya yanke hukumcin, wanda ya hana gudanar da kowace irin hidimar addini a yankin da ake takaddama a kan shi, wanda Musulmi da mabiya addinin Hindu, dukan su ke yin ikirarin cewa mallakinsu ne.

Masu kishin addinin Hindu sun shirya yin addu'o'i a jibi Jumma'a a wani kokarin da suke yi na neman gina wurin ibada a inda aka rushe Masallacin. Masu tsananin kishin addinin Hindu ne suka yi kaca-kaca da Masallacin a shekarar 1992, suna masu cewa an gina Masallacin ne a daidai inda aka haifi Rama, wanda suke bautawa.

Gardamar da ta kancame akan batun gina wurin ibadar ta haddasa tarzomar addini a kwanakin baya, al'amarin da ya hallaka mutane fiye da 700 a Jihar Gujarat dake yammacin kasar ta Indiya.

XS
SM
MD
LG