Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Commonwealth Tayi Tur Da Zaben Zimbabwe - 2002-03-14


Wata tawagar 'yan kallon zabe ta kungiyar "Commonwealth" tayi tur da zaben shugaban kasar da aka gudanar a Zimbabwe, matakin da watakila yana iya kaiwa a kore ta daga cikin wannan kungiya ta kasashen da Ingila tayi wa mulkin mallaka.

A cewar rahoton kungiyar, wannan zaben da shugaba Robert Mugabe ya lashe bai bayyana irin muradun masu jefa kuri'a na kasar ba. Ana sa ran samun cikakken rahoton wannan tawaga a cikin 'yan kwanakin dake tafe.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya ce ya samu rahotannin dake sabawa juna kan yadda aka gudanar da wannan zabe.

Amurka da Ingila da sauran kasashen turawa na yammacin duniya sun ce wannan zabe dai na magudi ne. Shi ma dan takarar adawa, Morgan Tsvangirai ya ki yarda da sakamakon zaben, yana mai cewa an tabka magudi.

Amma kuma 'yan kallon kasashen Afirka da dama da suka halarci wannan zabe sun ce an gudanar da shi tsakani da Allah.

XS
SM
MD
LG