Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dick Cheney Yana Tattaunawa A Kasar Yemen - 2002-03-14


Mataimakin shugaban Amurka, Dick Cheney, ya isa kasar Yemen yau, a ci gaba da rangadin wasu kasashen gabas ta tsakiya 11 da yake yi, domin tattauna batun yaki da ta'addanci da Amurka take yi wa jagoranci.

Mr. Cheney ya isa birnin Sanaa, babban birnin Yemen, ta cikin wani jirgin saman sojan Amurka karkashin wasu tsauraran matakan tsaro. Mataimakin shugaban Yemen, Abd-Rabbu Mansur, ya taryi Mr. Cheney a filin jiragen sama, inda nan da nan suka zarce zuwa wani dakin taro domin tattaunawa da shugaba Ali Abdullah Saleh.

Yanzu haka dai, jami'an Amurka suna nuna damuwa cewa, mai yiwuwa wasu daga cikin 'yan-ta'addar kungiyar al-Qa'ida da suke arcewa daga Afganistan, zasu yi kumajin fakewa a cikin tsaunukan kasar Yemen. Tuni, sojojin Amurka suka isa kasar, domin taimakawa dakarun gwamnati a farauto 'yan ta'addar al-Qa'ida dake kasar ta Yaman.

A jiya laraba a kasar Masar, mataimakin shugaban Amurka Cheney, ya ce, a mataki na gaba na yaki da ta'addanci, za a hana 'yan-ta'adda da gwamnatocin da suke mara masu, yi wa Amurka da kawayenta barazana.

Ana cigaba da yada jita-jita cewa, watakila Iraqi ta kasance, kasar da Amurka za ta darfafa nan gaba, a yakin da ake yi da ta'addanci. Shugaba Bush ya ce, ba zai kyale Iraqi ta yi wa makomar duniya barazana ba, ta hanyar kera makaman kare dangi.

XS
SM
MD
LG