Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kwango-Kinshasa Ta Jingine Tattaunawa - 2002-03-14


Gwamnatin Kwango-Kinshasa ta janye daga tattaunawar da ake yi game da makomar kasar, tana mai yin hujja da abinda ta kira hare-haren da 'yan tawaye da sojojin Rwanda suka kai kwanakin baya.

Mashawartan gwamnatin Kwango-Kinshasa a birnin Sun City dake Afirka ta Kudu, sun shaidawa Muryar Amurka cewa an kai hare-haren ne kusa da garin Mouniro a gabashin Kwango.

Kungiyar 'yan tawaye mai suna "Congolese Rally for Democracy" mai samun goyon bayan sojan Rwanda, ta musanta wannan zargi. Kungiyar ta ce da ma garin Mouniro yana hannunta ne, kuma tana kare kai ne kawai daga hare-haren sojojin gwamnati.

Mashawartan kungiyar sun shaidawa Muryar Amurka cewa gwamnati tana dokin tsinke tattaunawar ne a saboda babban amininta, shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe, ya sake lashe zabe. Amma jami'an gwamnati sun ce ba wai sun tsinke shawarwarin ba ne, kuma komai ya faru ma, zasu ci gaba da zama a birnin na Sun City.

A baya cikin watan nan aka fara tattaunawa, a bayan da wani kokari makamancin wannan ya wargaje a watan Oktobar bara.

Yakin Kwango Kinshasa, wanda kasashe shidda ke da hannu a ciki, ya faro a shekarar 1998. Rwanda da Uganda suna goyon bayan kungiyoyin 'yan tawaye. Ita ma Burundi tana da runduna karama a Kwango. Gwamnatin Kwango-Kinshasa kuma tana samun goyon bayan sojojin kasashen Angola da Zimbabwe.

An ce mutanen da suka mutu a wannan rikici za su iya kaiwa miliyan uku.

XS
SM
MD
LG