Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Rwanda Da Laifin Wargaza Kokarin Wanzar Da Zaman Lafiya - 2002-03-15


Wakilin kasar Faransa a Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya ce sojojin Rwanda su dubu 10 sun kai hari kan garin Moliro dake gabashin Kwango-Kinshasa, a wani matakin da ya bayyana a zaman mummunar koma-baya ga kokarin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Jakada Jean-David Levitte shi ya bayyana wannan yau Jumma'a a gaban Kwamitin Sulhun MDD a New York. A jiya alhamis Kwamitin Sulhun ya bukaci jakada Levitte da ya jagoranci wata tawagar neman zaman lafiya ta MDD zuwa yankin tsakiyar Afirka domin farfado da shirin wanzar ad zaman lafiya a Kwango-Kinshasa.

Amma kuma wani babban jami'in gwamnatin Rwanda, ya shaidawa Muryar Amurka cewa wannan zargi ba ya da madafa ko kadan. Babban jami'in kula da manufofin hulda da kasashen tsakiyar Afirka a gwamnatin Rwanda, Patrick Mazimpaka, ya shaidawa Muryar Amurka cewa sojojin kasarsa dake Kwango, ba su ma kusa da garin Moliro.

Jiya alhamis gwamnatin Kwango-Kinshasa ta jingine shiga cikin tattaunawar neman zaman lafiya da ake yi a Sun City a kasar Afirka ta Kudu, tana mai yin hujja da hari kan wannan gari dake gabashin kasar.

Rwanda tana daya daga cikin manyan masu goyon bayan 'yan tawayen dake yakar gwamnatin Kwango Kinshasa.

XS
SM
MD
LG