Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ANC Ta Ce Sakamakon Zaben Zimbabwe Na Halal Ne - 2002-03-15


Jam'iyyar dake mulkin Afirka ta Kudu, ta tofa albarkarta kan zaben shugaba Robert Mugabe da aka sake yi a Zimbabwe, wanda ya lashe zaben da kasashen yammaci suke ci gaba da korafin cewa na magudi ne kawai.

Wata sanarwar da jam'iyyar ANC ta bayar a yau Jumma'a, ta ce sakamakon zaben ya bayyana muradun al'ummar kasar Zimbabwe, duk da kura-kuran da aka gani a fili cikin tsarin zaben.

Har yanzu shugaba Thabo Mbeki bai fito ya ce uffan ba, kan rahotannin dake cewa gwamnatinsa tana kokarin shawo kan Mr. Mugabe domin ya kafa gwamnatin hadin kan kasa da magoya bayan abokin adawarsa. Rahotannin da aka buga a jaridun Afirka ta Kudu da na kasashen waje sun ce tuni har Mr. Mugabe yayi watsi da wannan shawara.

A halin da ake ciki, Shugaba Mugabe ya kafa sabuwar dokar garkame bakin kafofin yada labarai. Dokar ta bukaci 'yan jarida na cikin gida da su nemi iznin gudanar da aikinsu daga wurin wata hukumar da gwamnati ta kafa, ta kuma takaita irin ayyukan da wakilan kafofin yada labaran kasashen waje zasu gudanar cikin kasar.

Jami'an Nijeriya ma sun bayyana cewa zaben na makon jiya na Allah da Annabi ne, amma kasashen turawan yammacin duniya suna yin tur da abinda suka bayyana a zaman magudi na kin karawa.

A ranar lahadi za a rantsar da shugaba Mugabe a wani sabon wa'adi na biyar.

XS
SM
MD
LG