Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankokin Isra'ila Sun Janye Daga Ramallah - 2002-03-15


Isra'ila ta janye tankokinta na yaki daga Ramallah, birni mafi girma a yankin Yammacin kogin Jordan da sauran yankunan Falasdinawa da ta mamaye cikin 'yan kwanakin nan, yayin da wakilin Amurka Anthony Zinni yake ci gaba da kokarinsa na ganin an samu cimma tsagaita wuta.

A yanzu haka, Janar Zinni yana ganawa da shugaban Falasdinawa Yasser Arafat, a bayan da ya tattauna da jami'an Isra'ila.

Mazauna birnin Ramallah, sun fito daga cikin gidajensu domin auna irin mummunar barnar da sojojin Isra'ila suka yi musu cikin kwanaki ukun da suka yi suna mamaye da wannan gari.

Sojojin Isra'ila suna tsaye dab da wadannan garuruwan da suka janye daga ciki, sannan kuma har yanzu suna cikin wasu yankunan mulkin kai na falasdinawa.

Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa uku yau a Zirin Gaza.

XS
SM
MD
LG