Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Daukaka Kara Ta Shari'ar Musulunci Ta Saurari Batun Malama Safiya - 2002-03-18


Masu gabatar da kararraki sun roki wata kotun Shari'ar Musulunci a arewacin Nijeriya da ta tabbatar da hukumcin kisa ta hanyar jefewa da wata kotun ta yanke tun farko a kan wata mace da aka samu da laifin yin zina.

A yau Litinin a Sakkwato wannan kotun daukaka kara ta dage ci gaba da azama har sai ranar 25 ga watan nan na Maris, lokacin da zata bayyana hukumcinta kan daukaka karar da Safiya Hussaini ta yi.

A watan Oktobar bara, wata karamar kotun Shari'ar Musulunci ta yanke hukumcin, a bayan da ta samu Safiya Hussaini da laifin zina ta hanyar haihuwa ba tare da tana da miji ba.

Da farko Safiya ta ce an yi mata fyade ne, amma kuma daga baya sai ta janye wannan batu ta ce tsohon mijinta ne yayi mata ciki a bayan sun rabu.

Wannan hukumcin kisa ya janyo koke-koke daga kasashen waje tare da damuwa kan batun kare hakkin bil Adama a Nijeriya.

A can baya, shugaba Olusegun Obasanjo, mai bin addinin Kirista, ya bayyana cewar yana da kwarin guiwar matar zata yi nasara a kotun daukaka karar.

Wannan shine karon farko da aka yanke hukumcin kisa kan mace, tun lokacin da wasu jihohi 12 a Nijeriya suka sake bullo da yin aiki da dokokin Shari'ar Musulunci a cikin shekaru biyun da suka shige.

XS
SM
MD
LG