Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Hudu A Sabon Fada A Indiya - 2002-03-18


Sabon fada a tsakanin Hindu da Musulmi a Jihar Gujarat dake yammacin Indiya, yayi sanadin mutuwar mutane hudu.

A barkewar fada mafi muni da aka gani cikin makonni biyu, gungu-gungun mutane daga bangarorin, wadanda ba su ga maciji da juna, sun yi watsi da dokar hana yawon dare a birnin Ahmedabad, suka yi ta gwabzawa har zuwa asubahin yau.

A Baroda dake kudu da nan kuma, wasu 'yan tsageran addinin Hindu sun dabawa Musulmi biyu wuka suka kashe su a hannun 'yan sandan dake yi musu rakiya. Wasu mutanen biyu sun mutu a harbe-harben 'yan sanda.

Fada na baya-bayan nan ya biyo bayan tarzomar da aka yi a watan da ya shige a Jihar Gujarat, inda aka kashe mutane fiye da 700, akasarinsu Musulmi.

XS
SM
MD
LG