Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Amurka Yana Ganawa Da Firayim Ministan Isra'ila - 2002-03-18


Mataimakin shugaban Amurika Dick Cheney yana can Isra'ila, inda yake kara jaddada azamar da Amurka take yi wajen ganin an kulla wani shirin tsagaita wuta a tsakanin Isra'ila da Palasdinawa, domin a kawo karshen zubar da jinin da bangarorin biyu suka shafe watanni 18 suna yi.

Mr. Cheney yana ganawa da Firayim Ministan Isra'ila Ariel Sharon, amma banda jagoran Palasdinawa, Malam Yasser Arafat, wani mataki da ya hasala Palasdinawa.

A yau ne kuma, jakadan Amurka na musanman, Anthony Zinni, ya hada jami'an Isra'ila dana Palasdinawa wuri guda, domin su tattauna gameda batun janye sojojin Isra'ila daga yankunan ikon Palasdinawa da suka sake mamayewa cikin 'yan kwanakin nan.

Jami'ai daga bangarorin biyu sun yi tsokacin cewa, mai yiwuwa dakarun Isra'ila su fara janyewa daga yankin birnin Bethlehem a daren yau litinin.

XS
SM
MD
LG