Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Diflomasiyya Suna Zaune Cikin Shirin Ko-Ta-Kwana a Pakistan - 2002-03-18


Ma'aikatan diflomasiya da sauran cibiyoyin jakadancin kasashen waje na cikin shirin ko ta kwana a duk fadin kasar Pakistan, a daidai lokacin da hukumomin kasar ke kokarin farauto wadanda suka kai mummunan hari kan wata majami'ar 'yan darikar Protestant a Islamabad a jiya lahadi.

Harin da aka kai kusa da ofishin jakadancin Amurka da gurneti, ya hallaka mutane biyar Kiristoci a lokacin da suke ibada a majami'ar sannan kuma wasu mutane 45 suka jikkata.

Shugaban kasar Pakistan, Pervez Musharraf, ya bada umarnin daukan zafafan matakan farauto wadanda suka kai wannan hari haka kuma ya kira wani taron manyan jami'ai a gobe talata, in Allah Ya gwada mana, da nufin duba matakan tsaro a majami'ar da kuma sauran cibiyoyin jakadancin kasashen waje.

A jiya lahadi ministan cikin gidan kasar Pakistan, Moinuddin Haider, ya fada cewa a 'yan kwanakin baya jami'an majami'ar suka bukaci jami'an tsaron kasar ta Pakistan da su daina binciken mutanen dake shiga ciki, bayan da wasu masu zuwa ibada suka yi korafin cewa ana takura musu.

Ya zuwa yanzu dai babu wani mahalukin da ya fito ya dauki alhakin kai wannan hari.

XS
SM
MD
LG