Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cheney Ya Ce A Shirye Yake Ya Gana Da Arafat Idan Har... - 2002-03-19


Mataimakin shugaban Amurka, Dick Cheney, ya ce a shirye yake ya gana da shugaban Falasdinawa, Malam Yasser Arafat, nan bada jimawa ba, idan har ya yarda ya aiwatar da shirin tsagaita wutar da Amurka ta gabatar kwanakin baya domin kawo karshen tashin hankalin watanni 18 tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Mr. Cheney ya bayyana wannan a wurin wani taron 'yan jarida na hadin guiwa da firayim minista Ariel Sharon na kasar Bani Isra'ila, bayan da mutanen biyu suka tattauna yau talata a birnin al-Qudus.

Mataimakin shugaban ya ce zai iya ganawa da Malam Arafat idan har wakilin Amurka na musamman a yankin, Anthony Zinni, ya hakkake da cewa Falasdinawa sun tashi tsaye suna yin bakin kokarinsu domin aiwatar da shirin tsagaita wutar.

Mr. Sharon ya ce Isra'ila zata kyale Malam Arafat yayi zirga-zirga a waje idan har ya fara aiwatar da shirin.

Wani babban jami'in Falasdinawa, Nabil Abu Rudainah, ya bayyana furucin Mr. Cheney a zaman "matakin kwarai" a kokarin maido da hulda kyakkyawa a tsakanin Amurka da Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG