Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce Har yanzu Da Sauran Fada a Afghanistan - 2002-03-19


Shugaba Bush ya bayyana farmakin nan mai suna "Operation Anaconda" a Afghanistan a zaman nasara, amma kuma ya ce har yanzu ad sauran fada a gaba.

A lokacin da yake jawabi jiya litinin a wata masana'antar dake Jihar Missouri, Mr. Bush ya yabawa sojojin Amurka ya kuma gode musu a saboda gwabzawar da suka yi da mayakan al-Qa'ida da Taleban lokacin wannan farmaki na tsawon makonni biyu.

Har ila yau shugaban yayi kira ga majalisar dokoki da ta zartas da kasafin kudin da ya gabatar mata, wanda ya kunshi kari mai yawan gaske kan ayyukan soja.

A halin da ake ciki, sakataren tsaron Britaniya, Geoff Hoon, ya bada umurnin girka wasu zaratan sojojin kundumbala su dubu 1 da 700 a Afghanistan.

Har ila yau a jiya litinin, Birgediya Janar John Rosa na rundunar sojojin saman Amurka ya ce zaratan sojojin Amurka sun kashe mutane 16 da ake kyautata zaton mayakan al-Qa'ida ne, wadanda ke tafiya cikin wata kwambar da ake zaton tana neman tserewa ne zuwa Pakistan.

XS
SM
MD
LG