Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Madugun Adawar Zimbabwe Da Laifin Cin Amanar Kasa - 2002-03-21


Kwanaki kadan a bayan da shugaba Robert Mugabe ya kayar da shi a zaben da har yanzu ake gardamarsa, an tuhumi madugun adawa na Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, da laifin cin amanar kasa.

A yau laraba a Harare, babban birnin Zimbabwe, hukumomi suka tuhumi Mr. Tsvangirai a gaban kotu, tare da wani dan majalisar dokoki dan jam'iyyar adawa, dangane da makarkashiyar da aka yi zargin an kitsa ta kashe shugaba Mugabe. An bada belin mutanen biyu.

Mr. Tsvangirai, wanda yana iya fuskantar hukumcin kisa, ya fito da kakkausar harshe yana musanta wannan zargi. A baya cikin watan nan aka tuhumi mataimakin madugun 'yan adawar, Welshman Ncube, dangane da wannan makarkashiya da ake zargin an kulla.

A halin da ake ciki, Babbar Kungiyar Kwadago ta Kasar Zimbabwe ta kaddamar da yajin aikin kwanaki uku a fadin kasar, domin nuna rashin jin dadin yadda gwamnati take gallaza wa 'yan adawa. Masu fashin baki a birnin Harare sun ce wannan yajin aikin bai yi tasiri ba a babban birnin, inda ayyuka suka ci gaba da gudana kusan kamar yadda aka saba gani a yau da kullum, im ban da harkoki kadan da suka ragu.

Gwamnati ta ayyana wannan yajin aiki a zaman na haramun.

A jiya talata, wani kwamiti na musamman na Kungiyar "Commonwealth" ya dakatar da Zimbabwe na tsawon shekara guda daga cikin wannan kungiya ta kasashen da akasarinsu Ingila ta yi wa mulkin mallaka. Kungiyar mai wakilai 54 ta ce zaben shugaban kasa da aka yi cikin wannan wata a Zimbabwe, ba a yi shi tsakani da Allah ba.

XS
SM
MD
LG