Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Betty McCollum ta majalisar wakilan Amirka ta kare Safiya - 2002-03-22


INTRO: Yayinda labarin hukuncin Safiya da matsayin Ministan Shari’a Godwin Agabi cikin wata wasikar da ya aikewa gwamnonin jihohin da ake amfani da shari’a ya zama ruwan dare, anan Amirka wata ’yar majalisar wakilai daga jihar Minnesota ’yar jam’iyyar democrats, Betty McCollum ta gabatarda wata sanarwar da aka bugata a ranar Litnin 18 ga wata, wanda a ciki take suka akan matsayin hukuncin da aka yankewa Safiya. Wannan rahoto da na rubuta daga sanarwar tata ne da kuma hirar da Muryar Amrika ta yui da ita kai staye a gameda batun. TEXT: Betty McCollum bata bata lokaci ba wajen baiyana matsayinta a gameda hukuncin. Sakonni biyu ne kwarara suka fi fitowa daga matsayin ’yar majalisar ta wakilan Amirka wadda ta bada sanarwar gabatarda wani kuduri da zai la’anci hukuncin jifar mutun har sai ya mutu. Na farkonsu shine hukuncin kansa wanda ta ce tsananinsa ya wuce misali, sannan sai na biyu kuma wanda ta fi bada karfi akai. Watau yadda shari’ar ta nuna banbanci tareda gallazawa Safiya a saboda ita mace ce, tareda nuna fifiko da sakin wanda yayi mata cikin. Sanarwar ta ambaci cewa ‘ Shari’ar Safiya Husseini ya zama abin dagawa sama a duniya, cike da nasiha kan irin banbancin da mata suke fuskanta a dukkan fadin duniyar. Ta kara da cewa ‘sakon da nake neman aikewa shine cewa kowane mutun a duniyarnan ya cancanci girmamawa da bashi dama daidai da kowa, kuma kisa ta hanyar jifa ya sabawa matsayin kiyaye hakkin dan adam da kasashen duniya suka runguma.’ Kudurin McCollum ya bukaci shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da nan take ya dakatarda hukuncin kisan tareda tabbatarda duk wani hukunci ya dace da sharuddan kiyaye hakkin dan adam na kasa da kasa. Ta ce akwai wurare da dama a duniya da irin wannan banbanci yayi kamari, idan ana batun wulakanci da tozartar da ake nunawa mace. Ta ce tilas a tabbatarda cewa mata manya da diya mata a koawace kasar duniya suna fuskantar shari’a daya babu banbanci. ‘Yar majalisar McCollum ta ce zata daga murya wajen haskaka tareda faiyacewa rashin adalcin da mata ke fuskanta da danniya don kawai suna matan. Bayan sanarwar ce kuma........(Muryar Amirka) ta yi hira da McCollum. Inda aka tambayeta sakon da take neman aikewa. //McCollum act /// “WE WANNA WORK INTERNATIONALLY WITH.......... HADIZA: Muna son yin aiki da kasashen duniya domin mu tabbatarda cewa ba’a ci gaba da fuskantar banbanci na rashin adalci ga mata ba, kamar dai irin wanda wannan mace ke fuskanta. Na biyunsu shine cewa irin hukuncin yayi tsanani kuma na ba saban ba ne wanda ya keta matsayin kiyaye hakkin da aka cimma a duniya, kuma tilas a dakatar. END ACT. TEXT: Ko bayan haka Muryar Amirka ta tambaye ta ko yaya take daukar tsarin shari’ar ne ma baki daya, ko tana masa ganin abinda ya wuce yayinsa ne. //McCollum act/// “I WANT TO MAKE THIS CLEAR THAT THIS IS NOT........... HADIZA: Ina son baiyana muku a fili cewa wannan wani bangare ne na shari’a daya kawai, wanda ya sha banban da sauran tsarin. Ba wai mataki ne da ake yawaita gani ba a kasashen dake amfani da tsarin. A zahiri ma wannan irin hukunci ba a addinin Islama yayi asali ba, dinbin shekaru kafin sannan ake amfani da shi. Amma mu abinda muke fadi shine cewa duniya fa ta ci gaba, kuma tsarin gudanarwarta ya sauya, kama tun daga kiyaye hakki da tabbatarda adalci da kafa dokoki. Kuma duniya a yau bata rufe ido akan duk wani yunkurin nunawa kowa banbanci domin akwai yana mace. END ACT. TEXT: Ko bayan hakan an tambaye ta ko in baicin wannan tana da wata suka ne ga starin Shari’ar baki daya. Manufa ta baiyana matsayin kudurin ko sakonsa a dunkule, shin ko suka yake ga kasancewar tsarin shari’a a wannan zamani. //McCollum act/// “ I WANT TO REPEAT AGAIN THAT............. HADIZA: Ina son sake jaddadawa cewa wannan mataki ba yana sukan tsarin shari’ar Islama ne ba baki daya. Wannan mataki ne na baiyana ra’ayinmu akan wani abu da muke dauka a zaman keta hakkin dan adam. Kuma fatarmu ita ce kotun da zata kammala yanke matsayi akan wannan batu zata hangi matsayinmu ta amince cewa ya keta hakki. END ACT. TEXT: Betty McCollum dai kamar yadda muka ce ’yar jam’iyyar democrat ce daga mazaba ta hudu a jihar Minnesota. Tana wakiltar yanki mai muhimmanci da ya hada wasu kananan hukumomin biyu a tsakiya da Ramsey da Dakota, sannan da babban birnin jihar St. Paul. CART:.......BE REALISTIC....... - DOKA

XS
SM
MD
LG