Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Zasu Gana Yau a Abujar Nijeriya - 2002-03-25


A yau litinin, shugabannin kasashen Afrika za su yi wani taro a Nijeriya, domin tattaunawa gameda hanyoyin aiwatar da shirye-shiryen bunkasa harkokin tattalin arziki a nahiyar. Wannan taron koli na kwana biyu da za a gudanar a Abuja, babban birnin Nijeriyar, zai samu halartar shugabanni daga kasashe kusan 20.

Hukumar nan mai bullo da sabbin hanyoyin kawance domin bunkasa Afrika, N-E-P-A-D a takaice, ita ke daukar nauyin taron kolin. Yanzu haka dai, hukumar ta N-E-P-A-D tana kokarin ganin ana zuba jarin da zai kai na dala milyan dubu 64 a shekara a Afrika, da nufin farfado da tattalin arzikin nahiyar dake cikin garari.

Batutuwan da shugabannin za su tattauna kansu sun hada harda na zaman lafiya da tsaro, sai aikin gona, da walwalar kasuwanci, da kuma tsare-tsaren tattalin arziki.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya bada rahotan cewa tun a jiya lahadi, shugaban kasar Afrika ta Kudu, Thabo Mbeki, jigo a hidimar kirkiro da hukumar ta N-E-P-A-D, ya yi wata ganawar kut-da-kut, cikin sirri, shi da shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo.

Kasashen da za su halarci wannan taro na birnin Abuja sune: Senegal, Mali, Afrika ta Kudu, sai Botswana, da Mozambique,Cameroon, da jamhuriyar Congo, sai Gabon da Ethiopia da Mauritius, sai Rwanda, Algeria, Masar da Tunisia. Sauran sun hada da; kasar Tanzania, da Uganda, da Sao Tome da Principe sai Ghana da kuma masaukin baki, Nigeria.

Kodayake a cikin watan yuni, Firayim Ministan kasar Canada Jean Chretien, zai amshi bakuncin taron kolin kungiyar kasashen nan guda takwas da suka habaka, G-8 a takaice a Canadar, a ranar biyar ga watan aprilu ne kuma, Mr. Chretien zai tattauna da wasu shugabannin kasashen Afrika guda shida a Nijeriya.

XS
SM
MD
LG