Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bukin Ranar Cutar Fuka A Duniya - 2002-03-25


Hukumar Kiwon lafiya ta duniya ta gudanar da bukin ranar Cutar Fuka ko TB ta duniya jiya lahadi, ta hanyar kaddamar da gangamin shekara guda na hana yaduwar wannan mummunar cuta dake kashe mutane miliyan biyu a kowace shekara.

Taken da hukumar ta bai wa wannan gangamin shine “Hana Yaduwar Cutar Fuka, Yaki da Talauci ne” domin ta jaddada cewa yaki da wannan cuta zai wanzar da karuwar arziki a fadin duniya.

Jami'an kula da lafiyar jama'a sun yi kiyasin cewa ana bukatar dala miliyan dubu daya domin warkar da masu fama da wannan cuta tare da dakile yaduwarta a kasashe guda 22 wadanda ke dauke da akasarin masu fama da wannan cuta a duniya.

Wannan cuta ta fuka, cuta ce da ake ganinta sosai a kasashe masu tasowa, koda yake wani kwararre na hukumar kiwon lafiya ta duniya ya ce cutar tana sake kunno kai a kasashen duniya masu arzikin masana’antu.

XS
SM
MD
LG