Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Shari'ar Musulunci A Nijeriya Ta Saki Matar Da Aka Ce Za a Jefe - 2002-03-26


Wata kotun daukaka kara ta shari'ar Musulunci a arewacin Nijeriya, ta soke hukumcin kisa ta hanyar jefewa da aka yanke a kan wata macen da aka samu da laifin yin zina.

Wannan kotun daukaka kara dake birnin Sakkwato, a arewa maso yammacin Nijeriya, ta bada umurnin da a saki wannan mace mai suna Safiya Hussaini nan take, tana mai yin watsi da hukumcin bisa hujjoji na rashin bin ka'ida.

A watan Oktoban bara, wata karamar kotun Shari'ar Musulunci ta samu matar mai shekaru 35 da haihuwa, kuma mai 'ya'ya biyar, da laifin yin zina, a bayan da ta haihu ba tare da tana da aure ba.

Wannan hukumci ya janyo suka daga kasashen waje, tare da damuwa kan hakkin Bil Adama a Nijeriya.

Wannan hukumci na litinin din nan, wanda 'yan rajin kare hakkin Bil Adama suka yi marhabin da shi, ya zo a daidai lokacin da aka samu labarin cewa wata kotun ta Shari'a ta yanke hukumcin kisa ta hanyar jefewa kan wata matar dabam da aka samu da laifin yin zina.

Rahotanni sun ce wata kotu a garin Bakori dake Jihar Katsina ta yanke hukumcin kisa kan Amina Lawal Kurami a ranar Jumma'a. Tana da kwanaki talatin na daukaka karar wannan hukumci.

A makon da ya shige, gwamnatin tarayya a Nijeriya ta ce dokokin Shari'ar da ake aiwatarwa a jihohi 12 na arewacin kasar, sun sabawa tsarin mulki, ta kuma umurci gwamnonin jihohin da su watsar da Shari'a. Amma kuma, gwamnonin sun yi watsi da wannan umurni.

Daya daga cikin gwamnonin, Attahiru Bafarawa na Jihar Sakkwato, ya ce soke hukumcin da aka yanke kan Safiya Hussaini, ya nuna cewa Shari'ar Musulunci tana da tanade-tanade na mutunta hakkin dan Adam.

XS
SM
MD
LG