Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Sun Yarda Da Shirin Sa'udiyya - 2002-03-26


Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa dake ganawa a birnin Beirut, kafin taron kolin da shugabanninsu zasu yi a can, sun bayyana goyon bayansu ga shirin samar da zaman lafiyar da Sa'udiyya ta gabatar.

A litinin din nan, karamin ministan harkokin wajen kasar Kuwaiti, Sheikh Mohammed al-Sabah, ya ce har yanzu akwai bukatar tsara dalla-dallar shirin na Sa'udiyya. Amma ya ce yana sa ran taron kolin zai yi na'am da wannan shiri na Sa'udiyya, kuma zai zamo shawarar cimma zaman lafiya na kasashen larabawa baki daya.

Shirin yayi wa Isra'ila tayin kulla dangantaka da kasashen larabawa idan ta janye daga yankunan Larabawa da ta mamaye a yakin Gabas ta Tsakiya na 1967. Yarima Abdullahi, mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya, shine ya fara bayyana wannan shirin cikin wata hirar da yayi da jaridar New York Times a watan da ya shige.

Shugaban kungiyar kasashen larabawa, Amr Moussa, ya ce shirin na Sa'udiyya ya gabatar da zabi tsakanin adalci da zaman lafiya a gefe guda, da kuma fitina da rashin kwanciyar hankali a daya gefen.

Gobe laraba za a fara wannan taron koli na kasashen Larabawa, wanda zai samu halartar shugabanni da manyan jami'an kasashe 21 tare da jami'an hukumar mulkin kai ta Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG