Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Zai Gana Da Jami'an Iraqi Kan Sufetocin Makamai - 2002-03-26


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, yana shirin ganawa da ministan harkokin wajen Iraqi, Naji Sabri, a cikin wata mai zuwa, domin kara tattaunawa game da komawar sufetocin makamai na majalisar zuwa kasar ta Iraqi.

Kakakin Mr. Annan, Fred Eckhard, shi ya bada sanarwar wannan ganawa jiya litinin.

Ya ce Mr. Annan yana fata Iraqi zata bayyana cewa a shirye take ta yi aiki da umurnin majalisar na cewa a kyale sufetoci su koma kasar domin su binciki ko Iraqi tana da makamai na kare-dangi.

Mr. Annan da Malam Sabri sun gana ranar 7 ga watan Maris, a tattaunawar farko da aka yi tsakanin wani babban jami'in Iraqi da jami'an MDD cikin shekara guda.

Amurka ta ce ba ta tsammanin tattaunawar zata cimma wani abu, idan har ba wai Iraqi ta nuna cewa zata bai wa sufetocin iznin shiga duk inda suke son gani ba ne.

XS
SM
MD
LG