Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobe Alhamis Nijeriya Da Kamaru Zasu Gabatar Da Hujjojinsu Na Karshe Gaban Kotun Duniya - 2002-03-27


Idan Allah Ya kai mu gobe alhamis ne Nijeriya da Kamaru zasu gabatar da hujjojinsu na karshe gaban kotun duniya, kan rikicin da suka jima suna yi a yankin bakin iyakarsu.

Wannan shari'a da za a yi hukumcinta a Kotun Duniya dake birnin Hague, zata nemi warware rikicin da kasashen biyu suke yi, wanda ya kai su ga girka sojojinsu a yankin nan na Bakassi wanda aka ce yana da arzikin man fetur.

Wakilin Muryar Amurka a Afirka ta Yamma, Luis Ramirez, ya ce an yi wata guda cur ana sauraren shaida, inda kasashen biyu suka yi ta gabatar da hujjojinsu na mallakin wannan yanki na Bakassi, wanda wasu mutane suka yi imanin cewa yana dauke da arzikin mai da yawan gaske a kwance a karkashin kasa.

Kamaru tayi shekara da shekaru tana zargin Nijeriya da laifin mamaye wannan yankin na Bakassi da ta ce ba na Nijeriya ba ne, da kuma wani yankin kasa can wajejen Gamboru Ngala a kewayen tabkin Chadi.

A cikin karar da ta shigar a shekarar 1994, Kamaru ta bukaci Nijeriya da ta janye sojojinta daga yankin Bakassi, ta kuma biya kudin diyya ga gwamnatin Kamaru. Nijeriya ta mayar da martani ta hanyar cewa ya kamata Kamaru ta biya diyyar hare-haren da sojojin Kamaru suka kai.

A lokuta da dama cikin shekaru 9 da suka shige, sojojin kasashen biyu sun sha gwabzawa. Ba a tantance yawan mutanen da suka mutu a fadace-fadacen ba. Wani fadan ya barke a 1996, inda Nijeriya ta zargi sojojin Kamaru da laifin kai hare-hare, tare da raunata fararen hula da yawa.

Kasashen biyu sun yi musanyar fursunoni a shekarar 1998, amma har yanzu akwai zaman tankiya sosai tsakanin makwabtan biyu. Gwamnatin Nijeriya ta zargi Kamaru da laifin shirin fara binciken man fetur a yankin na Bakassi, abinda ya sabawa umurnin da kotun duniya ta bayar cewar kada wata daga cikin kasashen ta gudanar da wani aikin bincike a wannan yanki har sai bayan kotu ta warware rikicin mallakinsa.

A lokacin da ta shigar da wannan kara a shekarar 1994, gwamnatin Kamaru ta roki kotun da ta tantance bakin iyakar kasashen biyu ta teku da kuma ta doron kasa. A wancan lokacin dai, gwamnatin Nijeriya ta koka da matakin da Kamaru ta dauka na gabatar da wannan batu a gaban kotu, tana mai cewa kamata yayi a ce kasashen biyu sun warware duk wani sabanin dake tsakaninsu, su ya sunsu.

Wannan rikici ya samo asali fiye da shekaru 100 da suka shige a lokacin da Ingila da Faransa 'yan mulkin mallaka suka shata sabon bakin iyaka domin raba tsakanin yankunan da suka zamo Nijeriya da Kamaru.

XS
SM
MD
LG