Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Taron Kolin Abuja - 2002-03-27


Shugabanni da jami'ai daga kasashen Afirka fiye da dozin guda, sun kammala wani taro a Abuja, babban birnin tarayya Nijeriya, inda suka yarda da daukar sabbin matakan tabbatar da yin mulki bisa adalci a fadin nahiyar.

Wakilin Muryar Amurka ya ce taron na Abuja ya hada kan wakilan sabon shirin nan da ake kira Sabon Kawancen Raya Nahiyar Afirka, ko NEPAD a takaice.

Wannan shirin da ya kunshi kasashen arewacin Afirka, da wadanda ke kudu da hamadar Sahara, zai nemi karin agaji da sabbin jarurruka na miliyoyin daloli daga kasashen yammacin duniya.

Taron na Abuja, ya biyo bayan wani taron kolin Majalisar Dinkin Duniya da aka yi cikin watan nan a kasar Mexico, inda aka yanke shawarar kara yawan agaji ga kasashe masu tasowa wadanda suka aiwatar da muhimman sauye-sauyen tattalin arziki da na siyasa.

A bayan taron na jiya talata a Abuja, wakilan dake cikin wannan shiri sun bada sanarwar karshen taro dake cewa suna goyon bayan kirkiro da wani shiri ko tsarin da suka kira Daftarin Nazari da Tabbatar da Da'a na Afirka.

Wannan shiri ko tsari zai zamo tamkar ma'aunin dabi'u da take-taken shugabannin nahiyar, wanda kuma al'ummar Afirka ne zasu tsara, su gudanar tare da tabbatar da yin aiki da wannan daftarin da'a.

Shugabannin Afirka da suka gana jiya talata a Abuja suna fatan sabon kudurin da suka nuna na kyautata yanayin tattalin arziki da na siyasa a kasashensu, zai shawo kan kasashe masu arziki da su kara yawan agajin da suke bai wa nahiyar.

XS
SM
MD
LG