Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kananan Girgizar Kasa Da Cunkoson Ababen Hawa Suna Gurgunta Ayyukan Agaji a Afghanistan - 2002-03-27


Kananan girgizar kasa dake bin bayan babba tare da cunkoson ababen hawa suna gurgunta kokarin rarraba agaji a lardin Baghlan na arewacin Afghanistan, inda mutane dubu daya da 800 suka hallaka a girgizar kasar da aka yi ta yi ranar litinin da maraice.

Jami'an Afghanistan sun ce an tono gawarwakin mutanen dubu daya da 800 da suka mutu daga karkashin gine-ginen ad suka rusa kansu, suna masu fadin cewa har yanzu akwai wasu da dama dake binne a kasa. Jami'ai sun ce mutane kimanin dubu 4 suka ji rauni, yayin da gidaje dubu 10 suka lalace a lardin Baghlan, mai tazarar kilomita 120 a arewa da birnin kabul.

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun ce biyu daga cikin manyan hanyoyin mota uku na yankin sun lalace a sanadin girgizar kasar. An ci gaba da yin girgizar kasa har zuwa daren talata. Kamfanin dillancin labaran Reuta ya ce an samu cunkoson ababen hawa a kan hanyar Kabul zuwa inda aka yi girgizar kasar, a bayan da wasu manyan motoci biyu dake dauke da kayan agaji suka kife cikin ramin karkashin kasa na Salang.

Kungiyoyin agaji suna kokarin kai kaya, ciki har da tufafi, da barguna, da tanti, da abinci da jakunkunan laida na kunshe gawarwaki zuwa yankin da girgizar kasar tayi wa barna. Kungiyar agaji mai zaman kanta da ake kira "A.C.T.E.D" ta samu kaiwa yankin da aka yi girgizar jiya talata domin raba tanti 500 da barguna dubu daya da ake matykar bukata saboda sanyin hunturu.

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na Afghanistan, hamid Karzai, ya soke ziyarar da yayi niyyar kaiwa kasar Turkiyya domin ya jagoranci magance wannan bala'i.

XS
SM
MD
LG