Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 41 A Wata Arangama A Kasar Ghana - 2002-03-28


Hukumomin kasar Ghana sun ce an kashe mutane 41, cikinsu har da wani sarki, a wasu arangamomin da aka yi a tsakanin sassa masu gaba da juna a arewacin kasar.

'Yan sanda sun ce an fille kan Sarkin 'yan kabilar Dagomba, kuma jagoran zuriyar Andani, Ya-Na Yakubu Andani, a bayan da 'yan zuriyar Abudu masu gaba da shi suka kai farmaki cikin fadarsa jiya Laraba a garin Yendi, kilomita 530 a arewa da Accra, babban birnin kasar. 'Yan sanda sun ce an kona magoya bayan sarkin su 25 kurmus da ransu.

Wata majiyar ta 'yan sanda ta ce an samu wasu karin gawarwaki guda 15 a Yendi, kuma da alamun su ma an kashe su ne a wannan fada na kabilanci.

Gwamnatin Ghana ta kafa dokar hana yawo a Yendi, yayin da 'yan sanda da sojoji suke sintiri cikin garin.

Rahotanni sun ce tashin hankali ya barke a makon da ya shige a lokacin da 'yan zuriyar Abudu suka zagi manzon sarkin, wanda aka tura shi domin tattauna yadda jinsunan biyu na kabilar Dagomba zasu gudanar da babban bukinsu da ake kira Bugum.

Shi wannan buki na Bugum, ko wasan wuta, an shirya gudanar da shi tun a ranar talata, amma sai aka soke saboda zagin manzon sarki da kuma barkewar fada.

'Yan jinsi ko zuriyar Abudu, suna sarautar kabilar Dagomba, ta hanyar karba-karba tsakaninsu da 'yan jinsi ko zuriyar Andani.

XS
SM
MD
LG