Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaman Makoki Yau A Kasar Afghanistan - 2002-03-28


Yau alhamis ake zaman makoki a fadin kasar Afghanistan, domin tuna wadanda suka mutu a girgizar kasa mai karfin gaske da ta ratsa arewacin kasar ranar litinin.

Jiya laraba, shugaban gwamnatin riko, Hamid Karzai, ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da girgizar tayi wa barna a gundumar Nahrin dake lardin Baghlan, yayin da aka ci gaba da jin motsin kasa a yankin.

Har ila yau, ma'aikatan agaji suna fuskantar matsala a saboda rashin kyaun yanayi, da rashin hanyoyin ratsawa ta cikin duwatsun yankin da kuma barazana daga nakiyoyin dake binne a kasa.

Jami'an Afghanistan suka ce mutane har dubu biyu ne suka mutu a wannan girgizar kasa, wadda ta kai karfin awu 6 a ma'aunin motsin kasa na Richter. Amma kuma jami'an Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun ce a karshe za a gano cewa yawan wadanda suka mutu bai kai dubbai ba, watakila zai kama daga 800 ne zuwa dubu daya da 200.

MDD ta ce ma'aikatan agaji sun samu zarafin kai tantuna dubu 15 da ton 500 na abinci da barguna dubu 100 ga wadanda suka kubuta da rayukansu, duk da wahalar kaiwa gare su.

Garin Nahrin da wasu kauyuka da dama dake kusa da shi sun ji jiki sosai daga wannan girgizar kasa, inda akasarin gine-gine da gidaje suka rushe. A shekarar 1998 ma, wata girgizar kasar ta taba wannan yanki inda ta kashe dubban mutane.

XS
SM
MD
LG