Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 20 Sun Hallaka, Fiye Da 100 Suka Ji Rauni A Harin Kunar-Bakin-Wake - 2002-03-28


Harin kunar-bakin-wake da wani Bafalasdine ya kai a garin Netanya dake arewacin Isra'ila ya haddasa mutuwar mutum 20, ya raunata wasu fiye da 100.

Wannan hari na maraicen laraba, ya ragargaza wani hotel dake bakin teku, a daidai lokacin da dimbin baki suke layin shiga dakin cin abinci domin liyafar cin abincin kaddamar da bukin mako guda na kubutar kai na yahudawa, watau "Passover."

Kungiyar 'yan kishin Islama ta Hamas ta dauki alhakin kai harin.

Ofishin firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila, ya ce wannan harin bam ya nuna cewa shugabannin Falasdinawa ba su da niyyar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen watanni 18 da aka yi ana tashin hankali.

Mr. Sharon ya gana da manyan jami'an tsaronsa domin tattauna irin martanin da zasu iya maidawa.

Shugaba Bush na nan Amurka yayi tur da harin da kakkausar harshe, ya kuma nemi da a kawo karshen abinda ya kira "kashe-kashen rashin imani na babu gaira, babu dalili" a yankin gabas ta tsakiya. Mr. Bush ya ce tilas ne shugaban Falasdinawa, Malam Yasser Arafat, yayi bakin kokarinsa domin kawo karshen "kashe-kashen ta'addanci."

Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce yanzu ya zamo dole ga Malam Arafat ya bayyana a telebijin da rediyo ya fadawa Falasdinawa cewa tilas a kawo karshen hare-hare kan Isra'ila.

Mr. Powell ya ce ta'addanci yana lalata fatan da ake da shi na kafa kasar Falasdinu.

Har ila yau ya ce wakilin Amurka a Gabas ta Tsakiya, Anthony Zinni, zai ci gaba da zama a yankin bisa fatan kulla shirin tsagaita wuta a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG