Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Larabawa Zasu Ci Gaba Da Taron Kolinsu Yau Alhamis - 2002-03-28


Shugabannin kasashen Larabawa zasu koma ga taron kolin da suke yi yau alhamis a birnin Beirut tare da fatan cimma daidaiton ra'ayi kan shirin da Sa'udiyya ta gabatar na maidawa da larabawa yankunansu domin a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

An samu sabanin ra'ayi tsakanin wakilai a zaman taron na jiya laraba. Haka kuma, shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, da shugaba Hosni Mubarak na Misra da kuma SDarki Abdullahi na Jordan duk ba su samu damar zuwa taron ba.

Har ila yau, wakilan Falasdinawa sun fice daga zauren taron a saboda ba a nuna jawabin Malam Yasser Arafat a daidai lokacin da yake yinsa kamar yadda aka shirya ba. Za a nuna wannan jawabi yau alhamis.

A cikin jawabin nasa, Malam Arafat yayi tur da hare-haren ta'addanci kan fararen hula a rikicin da ake yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, amma kuma ya ce manufofin da gwamnatin Isra'ila take amfani da su a kan Falasdinawa, watau mamaye musu kasa, da rurrushe musu gidaje da birane, ta'addanci ne wanda ya fi wancan muni.

Malam Arafat ya kuma yaba da shirin na Sa'udiyya wanda yayi kira ga Isra'ila da ta janye daga yankunan da ta mamaye a yakin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967, su kuma larabawa su saka mata ta hanyar kulla dangantaka. Har ila yau wannan shiri na Sa'udiyya, wanda Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai suke goyon bayansa, yayi kiran da a bai wa Falasdinawa 'yan gudun hijira ikon komawa gidaje da garuruwansu a cikin Isra'ila.

Kasar Sham (Syria) tayi kira ga kasashen larabawa da su tsinke hulda da Isra'ila, su kuma goyi bayan tunzurin Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG