Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Wa Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Wa'adin watanni Shida A Saliyo - 2002-03-29


Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudurin da ya kara wa'adin aikin sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar Saliyo da wasu watannin shida. Manufa ita ce taimakawa kasar dake yankin Afirka ta Yamma ta farfado daga yakin basasar shekaru goma.

Jiya alhamis Kwamitin Sulhun ya zartas da cewa za a kara wa'adin aikin rundunar MDD a Saliyo mai suna "UNAMSIL" har zuwa ranar 30 ga watan Satumba. Gobe asabar wa'adin rundunar na yanzu zai kare.

Kwamitin ya roki gwamnatin Saliyo da ta gaggauta kokarin fadada ikonta a duk fadin kasar, musamman ma a yankunan da ake hakar duwatsun lu'ulu'u, wanda a da ya taimakawa 'yan tawaye wajen sayen makamai.

har ila yau, kwamitin yayi marhabin da kafa bangaren zabe a cikin rundunar ta "UNAMSIL" domin taimakawa Saliyo wajen shirya zaben 'yan majalisar dokoki da na shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga watan Mayu.

An kawo karshen yakin basasar Saliyo a watan Mayun bara, a lokacin da gwamnati da 'yan tawayen kungiyar R.U.F. (Revolutionary United Front) suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya. Amma kuma ba a ayyana karshen yakin ba sai a cikin watan Janairun nan da ya shige.

XS
SM
MD
LG