Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ce Tana Dari-Darin Yarjejeniyar Da Aka Kulla Tsakanin Iraqi Da Kuwaiti - 2002-03-29


Amurka tana bayyana dari-dari sosai da alkawarin da aka ce Iraqi tayi, cewar har abada ba zata sake kai harin mamaye makwabciyarta Kuwaiti ba.

Ranar alhamis aka samu labarin wannan sulhu tsakanin Iraqi da Kuwaiti a wurin taron kolin kasashen Larabawa a birnin Beirut. A karkashin yarjejeniyar, kasar Iraqi, wadda ta haddasa yakin yankin Gulf a bayan harin mamaye Kuwaiti da ta kai, ta yarda a rubuce cewar zata mutunta "diyauci da tsaron" kasar Kuwaiti.

Amma a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Richard Boucher, Iraqi ba ta taba nuna aniyar zahiri ta mutunta diyaucin Kuwaiti ba, ya kuma ce Iraqi ta sha karya alkawuran da tayi wa kasashen duniya.

Mr. Boucher ya ce gwajin zahiri na aniyar Iraqi zai fito ne ta hanyar take-takenta nan gaba, ba wai ta yin musafaha ba.

A wani matakin kuma na nuna cikakken hadin kai a tsakanin kasashen Larabawa, Yarima Abdullahi mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya, da babban wakilin Iraqi a taron kolin, Izzat Ibrahim al-Douri, sun yi musafaha, suka rungumi juna a lokacin da ake rufe taron kolin jiya alhamis.

Wannan mataki na nuna fatan alheri, shine karon farko da shugabannin kasashen biyu suka yi hulda da juna a bainar jama'a tun yakin Gulf na 1991.

Sa'udiyya ta tsinke huldar jakadanci da Iraq a bayan da ta mamaye Kuwaiti ta kuma yi barazana ga daular Sa'ud. Har yanzu ba a maido da huldar ba, amma kuma a cikin 'yan watannin nan ana kara kokarin maido da cikakkiyar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

XS
SM
MD
LG