Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaridar London Ta Ce Ta Samu Wasikar Gizo (Email) daga Wurin Osama bin Laden - 2002-03-29


Wata jaridar da ake bugawa da harshen Larabci a London ta ce ta samu wasikar gizo, watau Email, wadda tayi imanin cewa daga Osama bin Laden ne.

Editan jaridar mai suna al-Quds al-Arabi, Abdul-Bari Atwan, ya ce tsarin rubutu da lafazi na wannan wasikar gizo, sun yi kama da na wasikun baya da editan ya samu daga wurin madugun kungiyar al-Qa'ida ta ta'addanci da ake nema ruwa a jallo.

Amma editan ya ce ba ya da wata hanya ta tabbatar da ko wanene ya rubuta wasikar.

A cikin lafazi mai zafi, wasikar ta soki shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya wanda taron kolin kasashen larabawa yayi na'am da shi a Beirut.

Marubucin wasikar ya yaba da hare-haren kunar-bakin-wake da Falasdinawa ke kaiwa kan 'yan Isra'ila, yana mai cewa ana bukatar kowa da kowa ya rungumi Jihadi.

XS
SM
MD
LG