Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankokin Yakin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Ramallah - 2002-03-29


Jami'an tsaron Falasdinawa sun ce tankoki akalla 20 na Isra'ila sun kutsa cikin garin Ramallah, inda Isra'ila tayi wa shugaban falasdinawa Yasser Arafat talala tun cikin watan Disamba.

Suka ce an raunata Falasdinawa akalla 5 a gwabzawa da sojojin Isra'ila, a lokacin da wadannan tankoki suka yi tsinke wa ofishin malam Arafat daga kusurwoyi dabam-dabam.

Wannan mataki na Isra'ila ya zo a bayan da firayim ministan Bani Isra'ila, Ariel Sharon, ya kira taron majalisar tsaronsa cikin daren alhamis, domin tattauna irin matakan ramuwar gayyar da zasu iya dauka a bayan harin kunar-bakin-wake da wani Bafalasdine ya kai ranar laraba, ya kashe mutane 20 tare da kansa a garin Netanya.

Majiyoyin tsaron Isra'ila sun kuma an bukaci wasu sojojin wucin-gadi na Isra'ila da su shiga cikin damara.

Sa'o'i kafin wannan, shugaban Falasdinawa Yasser Arafat ya ce a shirye yake da a kulla shirin tsagaita wuta nan take. A bayan wannan ne kuma wani Bafalasdinen ya kashe yahudawa hudu 'yan kama-wuri-zauna a yankin Yammacin Kogin Jordan.

XS
SM
MD
LG