Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Democrat Suna Son Powell Ya Tafi Gabas Ta Tsakiya - 2002-04-01


Yayin da lamarin Gabas ta Tsakiya yake ci gaba da tabarbarewa, wasu jigogin jam'iyyar Democrat a majalisar dattijan Amurka sun yi kira ga sakataren harkokin waje, Colin Powell, da yayi tattaki zuwa yankin domin yayi kokarin wanzar da zaman lafiya.

Sanata Joseph Biden, dan jam'iyyar Democrat daga Jihar Delaware, ya shaidawa gidan telebijin na CBS jiya lahadi cewa yayi imani a kan lallai ne shugaba Bush ya dauki wani mataki na ba-zata. Mr. Biden ya ce tilas sakataren harkokin waje Powell ya nuna kwazo a fili tare da kasashen Larabawa.

Shi ma Sanata Joseph Lieberman na Jihar Connecticut, wanda ya bayyana a gidan telebijin na Fox, yayi kira ga Sakatare Powell da ya tafi yankin. Amma kuma ya ce bai kamata Amurka tayi kokarin hana Isra'ila kare kanta daga hare-haren kunar-bakin-wake ba. Lieberman ya kwatanta wadanda ke kai hare-haren da 'yan ta'addar da suka abka kan Cibiyar Cinikayya ta Duniya da Pentagon da jiragen sama a ranar 11 ga watan Satumba.

Arlen Specter, dan jam'iyyar Republican mai wakiltar Jihar Pennsylvania a majalisar dattijai, ya komo ke nan daga rangadin Gabas ta Tsakiya inda ya tattauna da shugaban Falasdinawa, Malam Yasser Arafat.

Ya shaidawa gidan telebijin na CBS cewar yayi imani babu yadda Malam Arafat zai iya shawo kan masu kai hare-haren bam na kunar-bakin-wake. Har ila yau ya ce ya goyi bayan tura sojojin Amurka marasa yawa zuwa Gabas ta Tsakiya, a wani bangare na rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasa da kasa idan an fara aiki da shirin tsagaita wuta.

XS
SM
MD
LG