Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Musulmin Duniya Suna Ganawa Yau A Malaysia - 2002-04-01


Ministocin harkokin wajen kasashen Musulmi zasu fara ganawa yau litinin a kasar Malaysia dominzana matsaya guda kan ta'addanci da abubuwan dake haddasa shi.

A bayan wannan, ana kyautata zaton wakilan kasashen 57 na Kungiyar Kasashen Musulmin Duniya, OIC, zasu caccaki lamirin Isra'ila a saboda farmakin da ta kai cikin yankunan Falasdinawa. Wannan taron kwanaki uku da za a yi a birnin Kuala Lumpur shine mafi girma da kasashen Musulmi zasu yi kan batun ta'addanci tun lokacin hare-haren 11 ga watan satumba a kan Amurka.

Ministan harkokin wajen Isra'ila, Syad Hamid Albar, ya ce Musulmi suna yin adawa da duk wani matakin alakanta addininsu da ta'addanci, suna kuma son a ringa binciken matsayin addinin kan duk wani batu. Har ila yau ya bayyana hare-haren da Isra'ila take kaiwa a kan hedkwatar Falasdinawa a Ramallah a zaman misali na ta'addancin gwamnatin wata kasa.

Shugabannin Musulmi sun ce babu ruwan addinin Musulunci da ta'addanci. Har ila yau sun kuma ce wasu daga cikin tashe-tashen hankulan da kasashen yammacin duniya ke dauka a zaman ta'addanci, gwahgwarmaya ce ta halal ta neman 'yanci ko ikon cin gashin kai, kamar irin gwagwarmayar da Falasdinawa ke yi.

XS
SM
MD
LG