Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afghanistan Zata Sanya Mata Masu Yawa Cikin Majalisa... - 2002-04-01


Jami'an Afghanistan sun ce shugabannin addini kwaya shida tak zasu bari, amma kuma zasu kyale mata har 150 su shiga cikin majalisar nan mai suna "Loya Jirga," watau majalisar shugabannin da zata zabi gwamnatin Afghanistan ta gaba.

Shugaban hukumar da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa kan zabe, ya bada sanarwa a ranar lahadi cewa tsohon sarkin Afghanistan, Mohammed Zahir Shah, zai koma kasar ranar 16 ga watan Afrilu domin fara shirya zaman wannan majalisa ta Loya Jirga.

Majalisar zata yi zama daga ranar 10 zuwa 16 ga watan Yuni.

Wakilai dubu 1 da 450 na wannan majalisa zasu fito daga kowane bangare na al'ummar Afghanistan. Tilas duk mai son shiga cikin majalisar ya kasance ba ya da alaka da ta'addanci, ko fataucin muggan kwayoyi ko kuma aikata wani laifi na yaki.

An ce tsoffin 'yan Taleban zasu iya neman shiga cikin majalisar idan har sun cika wadannan ka'idoji da aka shimfida.

Majalisar Loya Jirga, wadda al'ummar Afghanistan suka gaji kafawa daruruwan shekaru, zata zabi gwamnatin ad zata maye gurbin gwamnatin rikon kwarya ta Hamid Karzai.

XS
SM
MD
LG