Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Serbia Ta Bada Takardun Iznin Kamo Mukarraban Milosevic - 2002-04-01


Gwamnatin Serbia ta bada takardun iznin kama wasu mukarrabai hudu na tsohon shugaban Tarayyar Yugoslaviya, Slobodan Milosevic, ciki har da shugaban Jamhuriyar ta Serbia.

A jiya lahadi, gwamnatin ta tuhumi mutanen hudu da laifuffukan cin zarafin Bil Adama.

Ministan Shari'a na Serbia, Vladan Batic, ya ce 'yan sanda zasu yanke shawarar lokaci da kuma yadda zasu damke mutanen hudu, wadanda a yanzu ana iya mika su ga kotun duniya dake shari'ar laifuffukan yaki a birnin Hague.

Mutanen hudu sune shugaban Jamhuriyar Serbia, Milan Milutinovic; da tsohon mai bai wa Mr. Milosevic shawara kan harkokin tsaro, Nikola Sainovic; da tsohon kwamandan sojoji, Dragoljub Ojdanic; da kuma tsohon ministan harkokin cikin gida mai kula da 'yan sanda, Vlajko Stojiljkovic.

An bada takardun iznin kama su jim kadan kafin cikar wa'adin da Amurka ta bai wa Yugoslaviya na ta hada kai da kotun ta birnin Hague, ko kuma ta yi hasarar agajin kudi.

XS
SM
MD
LG