Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahara Sun Ragargaza Gadoji Biyu a Madagascar - 2002-04-02


Mahara sun ragargaza gadoji biyu jiya litinin a Madagascar, matakin da ya kara killace Antananarivo, babban birnin kasar, inda shugaban je-ka-na-yi-ka, Marc Ravalomanana, ya kafa gwamnati kishiyar ta halal.

Gidan rediyon Madagascar, wanda magoya bayan Ravalomanana suke gudanarwa, ya bada rahoton cewa an fasa gada guda a Miandriavazo, dayar kuma a Antinafotsy. Fasa wadannan gadoji biyu, ta biyo bayan lalata wata gadar a ranar Jumma'a.

Gwamnatin Ravalomanana ta dora laifin fashe-fashen a kan magoya bayan shugaba Didier Ratsiraka. Masu biyayya ga shugaba Ratsiraka sun yi makonni da katse hanyoyin motar da suka shiga cikin Antananarivo, matakin da ya katse jigilar kayan masarufin da ake matukar bukata a babban birnin.

Wannan fitina dai ta samo asali ne daga rikici kan zaben watan Disamba. Mr. Ravalomanana yayi imani da cewa shine ya lashe zaben kai tsaye, ya kuma zargi shugaba Ratsiraka da laifin yin magudi domin tilasta gudanar da zagaye na biyu an zaben fitar da gwani.

Shugaba Ratsiraka ya ce ba zai gana da abokin adawar nasa ba har sai shi Mr. Ravalomanana ya wargaza gwamnatinsa, ya kuma yarda da a gudanar da zagaye na biyu an zaben fitar da gwanin.

XS
SM
MD
LG