Wata kungiyar sojojin sa kai ta kafa gwamnati ta 'yan tawaye a kudu maso yammacin Somaliya, yanki na uku da ya bijirewa gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa a birnin Mogadishu.
'Ya'yan wannan kungiya mai suna "Rahanwein Resistance Army" sun sanyawa yankin nasu da sunan kasa mai zaman cin gashin kai na Kudu Maso Yammacin Somaliya. A jiya litinin kuma, suka nada shugaban soji, Kanar Hassan Mohammed Nur Shatigudud, a zaman shugabansu.
Somaliya ta kasa samun gwamnatin tarayya mai dorewa tun bayan faduwar gwamnatin marigayi Mohammad Siad Barre a shekarar 1991. An shirya gudanar da babban taron sasantawa na al'ummar Somaliya nan gaba cikin wannan wata a kasar Kenya.
Sauran yankuna masu cin agshin kansu da suka ayyana ballewa daga Somaliya sune Somaliland a arewa amso yammacin kasar, da kuma Puntland a arewa maso gabas.