Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Powell Ya Dage Batun Yanke Shawara Kan Bada Agaji Ga Yugoslaviya - 2002-04-02


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya dage batun yanke shawara kan ci gaba da bada agajin miliyoyin daloli ga kasar Yugoslaviya, har sai illa ma sha Allahu.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ya fada a jiya litinin cewa Mr. Powell "ya yanke shawara a kan cewa ba zai yanke shawara kan wannan batu" a yanzu ba. Har ila yau wannan matakin da ya dauka ya jefa Yugoslaviya cikin hadarin hasarar rancen kudi daga cibiyoyin kudi na kasa da kasa.

Gwamnatin Amurka ta dakatar da bada agaji ga Yugoslaviya da karfe 12 an daren lahadi, a bayan da hukumomin kasar suka kasa nuna karin hadin kai da kotun Majalisar Dinkin Duniya mai shari'ar laifuffukan yaki a birnin Hague.

A lokacin da ta yi wani taro jiya litinin, gwamnatin Yugoslaviya ta amince ba tare da hamayya ba, kan cewa zata hada kai da kotun, koda kuwa hakan yana nufin mika mutanen da ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki.

XS
SM
MD
LG