Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Ya Ce Har Yanzu Da Sauran Rina A Kaba a Rikicin Isra'ila Da Falasdinawa - 2002-04-02


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, yayi gargadin cewa rikicin Isra'ila da Falasdinawa zai kara yin muni nan gaba, sai fa idan a cewarsa, "an karya lagon akidar yaki."

Amma kuma, Mr. Annnan ya ce ba za a iya kawo karshen tashin hankalin da ya ki ci, ya ki cinyewa ba, har sai an takali muhimman batutuwan dake addabar sassan baki daya. Ya bayyana wadannan batutuwa a zaman mamayar da Isra'ila tayi wa yankunan Falasdinawa, tashin hankali, ta'addanci, da kuma fatarar dake addabar Falasdinawa.

Ya ce mutum maras hankali ne kawai zai iya fadin cewa wannan rikici ba zai kara muni ba.

Babban sakataren yayi wannan furuci nasa ne ga wakilan Kwamitin Sulhun majalisar a wani zaman sirri da suka yi jiya litinin.

A ranar asabar, Kwamitin Sulhun ya zartas ad wani kudurin dake yin kira ga Isra'ila da ta janye daga dukkan biranen Falasdinawa, sannan kuma dukkan sassan su rungumi shirin tsagaita wuta nan take.

XS
SM
MD
LG