Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Jami'in Tsaron Amurka Dake Kula Da Nahiyar Afirka Zai Yi Tattaki Zuwa Angola - 2002-04-03


Babban jami'in dake kula da harkokin Afirka a ma'aikatar tsaron Amurka, zai yi tattaki zuwa kasar Angola a cikin wannan watan, bisa fatan cewa za a iya wanzar da zaman lafiya a kasar, a bayan mutuwar madugun 'yan tawaye, Jonas Savimbi.

Wakilin Muryar Amurka ya ce mataimakin sakataren tsaro mai kula da Afirka, Michael Westphal, zai kai ziyararsa ta farko zuwa kasar Angola, tun hawarsa kan wannan kujera a karshen shekarar da ta shige. Har ila yau, ziyarar zata dauke shi zuwa Kwango-Kinshasa da Rwanda da kuma Burundi.

Mr. Westphal ya ce wannan ziyara tasa kusan ta bude idanu ce. Amma kuma ya shaidawa 'yan jarida a ma'aikatar tsaro cewa, wannan lokacin yana da muhimmanci a saboda Angola tana dab da sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da 'yan tawayen UNITA, yana mai cewa...

ACT: WESTPHAL: “For the longest time, we’ve been trying to work past the war. It seems that maybe we....”

FASSARA: Mun jima sosai muna kokarin ganin an kawo karshen wannan yaki. A yanzu, akwai alamar cewa muna da dama ta kawo karshensa. An tsara shirin tsagaita wuta, kuma ana tsammanin amincewa da shi gobe alhamis, 4 ga watan Afrilu a Luanda. Ni dai ba ni da wani takamammen aikin da zai kai ni can. Ba ni da wani takamammen sakon da zan kai can. Amma kuma zan dauki wannan dama ta ziyarar domin tattaunawa da rundunar sojojin Angola, zan kuma dauki damar tattaunawa da shugabannin UNITA. END ACT

IBRAHIM: Amma kuma, Mr. Westphal ya amince da cewa tuni har ya tuntubi wakilan 'yan tawaye, koda yake ya ki ya bayyana wanda yayi wa magana, ko kuma abinda suka tattauna kai. Irin wannan huldar da mutumin da ya gada yayi, ta haddasa rikici a saboda manufar Amurka wadda ta hanawa jami'ai ganawa da UNITA. Amma Mr. Westphal ya ce zamani ya canja, kuma sadarwa tana da matukar muhimmanci a wannan lokaci.

ACT: WESTPHAL: “They (UNITA) have called. They've called other people, also within the State Department. And to be quite honest, now is the time for....”

FASSARA: ('Yan UNITA) Sun kira mu. Sun kuma kira wasu mutanen a ma'aikatar harkokin waje. A gaskiya, yanzu lokaci ne na tuntubar dukkan sassan. Tilas UNITA ta samu damar sauya akidarta, daga rundunar soja ta koma kungiya ko jam'iyyar siyasa. Zasu iya yin haka ne kuwa ta hanyar sadarwa, a tsakanin su ya sunsu, da kuma tsakaninsu da wasu a waje, ciki har da mu. END ACT

IBRAHIM: Mr. Westphal ya nuna bacin rai da aka ce tuntubar UNITA tamkar tuntubar kungiyar 'yan ta'adda ce. Ya ce Amurka ba ta taba bayyana kungiyar UNITA a zaman kungiyar 'yan ta'adda ba. Ya ce lokaci yayi na mancewa da irin abubuwan bacin rai na shekara da shekarun da aka yi ana yakin basasa a Angola.

Kafin ya je shi ma'aikatar tsaro, Mr. Westphal yayi aiki a Kwamitin Hulda da Kasashen Waje na Majalisar dattijai a zaman mai kula da harkokin kasashen kudu da hamadar Sahara da kuma ayyukan kiyaye zaman lafiya. Har ila yau, tsohon sojan kundumbalar Amurka ne.

XS
SM
MD
LG