Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Wa'adin Tsayar Da 'Yan Takarar Shugaban Kasa A Saliyo - 2002-04-03


Al'ummar Saliyo zasu kara zaman jiran kwana guda kafin su san mutanen da zasu yi takarar kujerar shugabancin kasar a zaben da za a yi cikin wata mai zuwa. Zaben na ranar 14 ga watan Mayu, shine na farko da za a yi a kasar tun bayan yakin basasar shekaru 10.

Wakilinmu Muryar Amurka a yankin Afirka ta Yamma, Luis Ramirez, ya ce tun da fari, jiya talata ne cikar wa'adin da aka bai wa jam'iyyun siyasa a Saliyo na tsaida 'yan takararsu. Amma sai aka kara kwana guda zuwa yau laraba, a bayan da jami'an tsohuwar kungiyar 'yan tawaye ta RUF suka bayyana jiya talata da maraice a hedkwatar hukumar zabe a birnin Freetwon, suna rokon da a kara musu wa'adi.

Shugabannin RUF sun ce har yanzu ba su tsaida shawarar ko wanene zai yi musu takara ba.

Wannan kungiya, wanda a yanzu ake kira jam'iyyar RUFP (Revolutionary United Front Party), ta haddasa tsammanin warabbuka a kan ko wanene zata tsaida yayi mata takara. Shugaban kungiyar, Foday Sankoh, yana kurkuku, kuma a bisa dukkan alamu zai shafe wata da watanni masu zuwa a ciki. Amma jami'an RUFP sun ce suna daukarsa a zaman dan takararsu a zaben shugaban kasar. A makon jiya, shugaban hukumar zabe ta Saliyo, Walter Nicol, ya ce Mr. Sankoh ba zai iya yin takara ba, saboda bai yi rajistar jefa kuri'a ba.

Lauyoyin gwamnatin Saliyo sun tuhumi Mr. Sankoh da laifin kisan kai da wasu laifuffukan. Wannan tuhuma ta samo asali a watan Mayun 2000, lokacin da masu gadinsa suka bude wuta a kan 'yan zanga-zanga a kofar gidansa, har suka kashe mutane 20. Jami'ai sun ce Mr. Sankoh zai ci gaba da zama a kurkuku har sai an gama shari'arsa.

Har ila yau ana sa ran za a tuhume shi a gaban wata kotun Majalisar Dinkin Duniya ta musamman da zata yi shari'ar mutanen da ake zargi da laifin cin zarafin Bil Adama a lokacin yakin basasar.

Mutane sun fi tsammanin cewa shugaban kasar na yanzu, Ahmed Tejan Kabbah, shine za a sake zabe. Jam'iyyarsa ta SLPP ta samu goyon bayan jam'iyyar PDP wadda ke da rinjaye a majalisar dokoki. Masu fashin baki sun ce zaben ranar 14 ga watan Mayu zai zamo tamkar mizanin gwajin ko zaman lafiya ya dawwama a Saliyo, bayan mummunan yakin basasar da ya dauki ran dubun dubatan mutane, ya jikkata wasu dubban.

An ayyana samun zaman lafiya a kasar cikin watan Janairu, bayan sojoji fiye da dubu 40 sun mika makamansu a karkashin wani shirin MDD na kwance damarar yaki da aka fara aiki da shi a watan Mayun bara.

XS
SM
MD
LG