Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Taron Kasashen Musulmi a Malaysia Tare Da Fito Da Takardar Ayyanawa - 2002-04-03


Jakadu daga akasarin kasashen Musulmi sun kammala wani taron kwana uku a kasar Malaysia, tare da ayyana cewa, gwagwarmayar da Falasdinawa suke yi ta neman kafa kasarsu ba ta'addanci ba ne.

Cikin wani kundin bayanai mai kunshe da shafuka biyar da suka fitar yau laraba, ministocin harkokin waje da manyan jami'ai daga kasashe 57 na Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya, watau OIC a takaice, sun ce farmakin kunar-bakin-wake da Falasdinawa suke kaiwa, martani ne ga ta'addancin da Isra'ila take yi a yankunan Falasdinun da ta mamaye.

A cikin wannan kundi ko daftari wanda aka lakabawa sunan "Ayyanawar Kuala Lumpur" jakadun sun ce, suna yin Allah wadai da ko wane nau'in ta'addanci.

Ministan harkokin wajen Malaysia Syed Hamid Albar ya ce, wannan matsayi da suka ayyana, yana bada karin haske gameda abinda ya baiyana da cewa azamar kungiyar kasahen musulmi ta OIC ta ganin ta shawo kan ta'addanci. Ya kara da cewa, ba za iya alakanta ta'addanci da wata al'ada, ko tarihin zaman rayuwa, ko kuma wani addini ba.

Tun da farko dama, sai da wakilai a taron suka yi fatali da batun danganta ta'addanci da addinin Islama, ko kuma musulmi.

Koda yake jakadun sun yi alkawarin yin bayani filla-filla gameda abinda ake nufi da ta'addanci da abinda ke haddasa shi a lokacin wannan taro, amma sun gaza cimma daidaituwa ga wata fassara guda daya.

Alal misali, FIrayim ministan Malaysia, Mahatir Muhammad, ya ce, a ra'ayinsa za a iya fassara ta'addanci a zaman dukkan wani hari da za a kaiwa jama'a farar hula.

Amma Falasdinawa da wasu wakilan daga kasashen Gabas ta Tsakiya sun ki yarda da hakan. A dangane da haka ne, mahalarta wannan taro suka ce, yanzu majalisar dinkin duniya ce kawai wurin da ya fi dacewa a bullo da ma’anar wannan kalma "ta'addanci."

XS
SM
MD
LG