Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Yin Zanga-Zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinawa A Duk Fadin Yankin Gabas Ta Tsakiya - 2002-04-04


Dubban larabawa sun yi zanga-zanga jiya laraba a fadin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, domin yin tur da kutsawar baya-bayan nan da Isra'ila tayi cikin yankunan Falasdinawa tare da yin talala wa shugabansu, Yasser Arafat.

Zanga-zangar da aka yi a kofar ofishin jakadancin Amurka dake birnin Beirut ta rikide ta koma tashin hankali, inda 'yan sandan kwantar da tarzoma suka yi amfani da barkonon tsohuwa, da kulakai da kuma ruwa domin tare dubban 'yan zanga-zanga. 'Yan zanga-zangar sun taru domin yin tur da goyon bayan da ake zargin Amurka tana bai wa farmakin na Isra'ila. An raunata mutane da yawa, ciki har da jami'an tsaro da dama.

Har ila yau, xzanga-zangar nuna kin jinin Bani Isra'ila ta barke a manyan biranen Masar, Iraqi, Iran, Jordan, Yemen, Tunisiya da Qatar. Har ila yau an gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa a kasashen nahiyar Turai, ciki har da birnin Paris da birnin Marseilles a kudancin Faransa.

A can wani gefen kuma, Masar ta zabtare huldarta da Isra'ila im ban da wadda ta shafi Falasdinawa kai tsaye, domin nuna bacin ranta da irin take-taken Isra'ila a wannan rikicin.

An ambaci shugaban Falasdinawa Yasser Arafat yana mai yabawa da wannan matakin, yana kuma fadin cewa wannan gargadi ne ga Isra'ila. Amurka tayi kira ga Masar da Isra'ila da su ci gaba da yin huldar kut da kut duk da wannan tashin hankali dake kara yin muni.

XS
SM
MD
LG