Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kolin Wanzar Da Zaman Lafiya A Kwango Kinshasa Yayi Kiran A Janye Sojojin Kasashen Waje - 2002-04-04


An kammala wani taron kolin shugabannin yanki da aka shirya da nufin kawo karshen yakin da ake yi a Kwango Kinshasa, inda aka yi kiran da a janye dukkan sojojin kasashen waje daga wannan tsohuwar kasar Zaire.

Shugabannin kasashen Afirka 6 sun gana domin yin taron kolin na kwana guda a Lusaka, babban birnin Zambiya, inda suka tattauna wannan yaki da aka shafe shekaru uku da rabi ana gwabza shi.

Shugabannin kasashen Kwango Kinshasa, Afirka ta Kudu, Namibiya, Rwanda da Zimbabwe sun halarci wannan taro. Uganda ta tura ministan harkokin wajenta, yayin da Angola ta tura ministan tsaronta zuwa zauren taron.

A cikin sanarwar bayan taron da suka rarraba, shugabannin sun ce sun yarda cewar ya kamata a gaggauta janye sojojin kasashen waje. Har ila yau sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta girka sojojin kiyaye zaman lafiya kafin a janye sojojin na kasashen waje.

Wannan yakin da aka faro a shekarar 1998, ya shafi sojojin kasashe 6, ya kuma lankwame rayukan mutane miliyan biyu da rabi.

XS
SM
MD
LG