Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Shiga Nablus - 2002-04-04


Sojojin Isra'ila sun danna sun shiga Nablus, birni mafi girma a yankin Yammacin kogin Jordan, a daidai lokacin da Isra'ila ta shiga kwana na bakwai da fara kai hari kan Falasdinawa 'yan gwagwarmayar kwatar 'yancin kai.

An bada rahoton cewa yayin da ake caba kazamin fada, sojojin Isra'ila da tankokinsu na yaki suka isa tsakiyar birnin Nablus, sannan suka kewaye wasu sansanoni ukku na 'yan gudun hijira wadanda ke dab da wurin.

Hukumar mulkin kan Falasdinawa ta yiwa Falasdinawa kiran da su ja damara, su yi shirin yin abun da ta kira "gwagwarmayar sai baba-ta-gani" game da mamayewar da Isra'ila ta yi musu.

Tun daga ranar juma'ar da ta gabata, Isra'ila ta sake mamaye garuruwa takwas na yankin Yammacin kogin Jordan a cikin sumamen da ta ce tana yi ne da nufin kakkabe 'yan ta'adda.

A garin Bethlehem, sojojin Isra'ila sun ci gaba da yin kawanya ga Falasdinawa 'yan bindiga su fiye da dari wadanda suka fake a cikin wata majami'a.

An ce ana ci gaba da tattaunawa domin a kawo karshen wannan kiki-kaka ta kwanaki biyu a majami'ar.

XS
SM
MD
LG