Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Masu Arzikin Man Fetur Sun Ki Yarda Da Shawarar Iraqi - 2002-04-04


Manyan kasashe masu arzikin man fetur sun ki yarda da shawarar da Iraqi ta gabatar, cewar su daina saidawa da Amurka mai, a zaman wata hanya ta matsa mata lambar janye goyon bayan da take bai wa Isra'ila.

Iraqi ta fada a ranar talata cewa a shirye take ta dakatar da saidawa da Amurka danyen man fetur tare da kasar Iran da duk wata kasar Musulmin da ta yarda.

Amma ministan harkokin wajen Sa'udiyya, Sa'ud al-Faisal, ya shaidawa jaridar "Le Monde" ta Faransa cewa kasashen Larabawa ba zasu dakatar da saida man ga Amurka ba.

Indonesiya ta ce wannan ra'ayi ba mai yiwuwa ba ne, yayin da ita ma kasar Kuwaiti ta ki yarda da shi.

A ranar talata, farashin danyen mai ya cira sama sosai zuwa matsayin da bai kai ba cikin watanni shidan da suka shige a saboda fargabar cewa za a iya garkamawa Amurka takunkumin mai. Amma farashin ya sauko kasa kadan a jiya laraba.

XS
SM
MD
LG